Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Yi Barazanar Maida Martani Akan Amurka


China ta yi barazanar maida martani akan Amurka, bayan wani mataki da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka, na soma shafe matsayi na musamman da Hong Kong take da shi, da kuma saka dokoki masu tsauri akan daliban kasar China da ke Amurka. Matakin na Trump ya zo ne sakamakon sabuwar dokar tsaron kasa ta China akan Hong Kong.

Da ya ke magana da manema labarai a yau Litinin, mai magana da yawun Ministan Harkokin Wajen China, Zhao Lijian, ya ce “Sanarwar daukar wannan matakin ta taba lamuran cikin gidan China, kana za ta wargaza dangantakar da ke tsakanin Amurka da China, ta lalata dangantakar Amurka da China, kuma hakan zai cutar da kasashen biyu. China ba ta amince da matakin ba," ya kuma kara da cewar “Duk China za ta maida martani akan duk wasu kalamai ko mataki da Amurka ta dauka da zai shafi ra’ayin China.”

A ranar Juma’a da ta gabata Trump ya bayyana cewar wannan sabuwar dokar tsaron ta China akan kasar Hong Kong tana da illa sosai ga mutanen Hong Kong, haka kuma ta sabawa alkawarin China na mutunta ‘yancin birnin.

Ya kara da cewar China ta dade tana wargaza dadadden matsayin da martabar birnin.

A makon da ya gabata Majalisar kasar China ta kada kuri’ar amincewa da sabuwar dokar tsaron kasa akan Hong Kong, wadda ta haramta mata ballewa, da kuma abin da ta kira shisshigin kasashen waje da aikin ta’addanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG