Kafofin yada labaran China sun bada labarin an nada mataimakin shugaban kasan China Xi Jinping, mataimakin shugaban majalisar soja mai karfin gaske,hakan ya kara tabbacin watakil zai kasance magajin shugaban kasa Hu Jintao.
Yau litinin ce aka bada labarin Karin girman,a karshen taron shekara shekara na jam’iyyar gurguzu mai mulkin kasar da aka yi kwana hudu ana yi.
haka kuma ‘yan Jam’iyyar sun amince da shirin bunkasa tattalin arziki kasar sosai cikin shekaru biyar,amma cikin tsanaki.
Xi, yana bin sawun shugaban kasar a shiga majalisar sojojin,inda su biyun kadai ne farar hula.
Tun 2007 ne Mr. Jinping, yake wakili a majalisar gudanarwar Jam’iyyar.
Ana sa ran Mr. Hu zai yi murabus daga mukaninsa na shugaban Jam’iyyar a 2012.