Kasar China ta kawo karshen killace Wuhan, birnin da ke dauke da mutum miliyan 11, inda nan ne aka fara samun bullar cutar Coronavirus a watan Disambar bara.
Killacewar ta tsawon kwanaki 76, ta zo karshe ne jim kadan bayan karfe 12 na daren jiya Talata.
Matakin na zuwa ne bayan da alkaluman gwamnatin China na baya-bayan nan suka nuna cewa, babu wani sabon kamuwa da cutar,.
Har ila yau matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna shakku kan sahihancin alkaluman da gwamnatin kasar ta China ta fitar kan annobar cutar ta coronavirus.
A yanzu an amince mazauna birnin yin zirga-zirga ba tare da neman izini ba, muddin manhajar wayar hannu da aka wajabta amfani da ita, ba ta nuna cewa suna dauke da cutar ta COVID 19 ba.
Facebook Forum