Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea ta Yi ma Arsenal Dukan Kawo Wuka - 22/03/2014


Mohammed Salah na Chelsea, a bayan da ya jefa kwallo na 6 a ragar 'yan Arsenal
Mohammed Salah na Chelsea, a bayan da ya jefa kwallo na 6 a ragar 'yan Arsenal
A wannan rana da Arsene Wenger ke koyar da wasa na dubu daya ma Arsenal, Jose Mourinho da 'yan Chelsea sun kunyata su fiye da kima.

Chelsea ta lallasa abokiyar hamayyarta ta tsallaken titi a London yau asabar a filin wasa na Stamford Bridge, yayin da Jose Mourinho da 'yan wasansa, suka aike da sako cikin babbar murya ga sauran masu hankoron kamo su a gasar firimiya ta Ingila cewa su fa ba kanwar lasa ba ne.

Wannan shi ne karon farko a tarihi da Chelsea take doke Arsenal da ci 6 da babu.

Kai, a cikin minti 10 na fara wasan ma 'yan wasan na Chelsea suka fara nakkasa 'yan Arsenal, domin Samuel Eto'o da Andre Schurrle sun jefa kwallaye biyu. A minti na 16, Eden Hazard ya jefa kwallo na uku a wani bugun fenaritin da ya janyo hura hanci. Abinda ya faru shi ne Alex Oxlade-Chamberlain ya taba kwallon farko da Hazard ya buga da hannu, sai alkalin wasa ya gani ya hura bugun fenariti. Amma kuma sai yayi kuskueren korar Kierran Gibbs daga wasan domin ya zaci shi ne ya taba kwallon da hannu.

Wannan kuma rana ce da Arsene Wenger, manajan Arsenal yake yin abin tarihi, yana koyar da wasansa na dubu 1, amma sai wannan rana ta zamo abar kunya gare shi. kafin a tafi hurtun rabin lokaci, Oscar ya jefa kwallo na hudu, ana komowa kuma ya kara guda. Mohammed Salah ya jefa kwallo na shida kuma na karshe a ragar Arsenal.

Yanzu Chelsea ta kara ratarta a saman teburinw asannin firimiya na Ingila zuwa maki 7. Chelsea na da maki 69, yayin da 'yan Arsenal suke na uku da maki 62.
XS
SM
MD
LG