Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Catherine, Gimbiyar Wales Ta Bayyana Cewar An Gano Tana Da Cutar Sankara


Catherine, Gimbiyar Wales
Catherine, Gimbiyar Wales

Gimbiyar Wales ta sanarda cewar ta kamu da cutar sankara, harma an fara yi mata magani, inda ta bukaci al'umma su bata lokaci da wuri ta kammala samun waraka a killace.

WASHINGTON DC - Kate, kamar yadda aka fi saninta, tace gano cutar sankarar bayan kammala wani aikin tiyata a cikinta a watan janairun daya gabata yayi matukar girgizata amma tana dada samun sauki da murmurewa har kullum.

Duk da dai Gimbiyar, mai shekaru 42 da haihuwa, bata fayyace kowace irin sankarar ke damunta ba, saidai ta bayyana 'yan watanniin baya-bayan nan tun bayan data kwanta a asibiti a matsayin masu tsananin gaske a gareta da iyalinta.

A cikin wani faifan bidiyo da aka nada a fadar Windsor a Larabar da ta gabata, Gimbiyar ta kara da cewar, "an gudanar da wani gagarumin aikin tiyata akai na a birnin Landan a watan Janairun daya gabata, kuma a lokacin ba'a zaci cewar larurar tawa sankara ce ba.

"An samu nasara a aikin tiyatar. saidai, gwaje-gwajen da aka gudanar sun nuna cewar akwai sankara a jikina".

"Don haka tawagar likitocina suka bada shawarar a fara yi min magani da sinadarai a matakin rigakafi kuma zangon farko na karbar magani".

Ganin karshe da aka yi mata a bainar jama'a shine a ranar 25 ga watan disambar daya gabata, inda ta hadu da sirikinta Sarki charles na 3 da sauran manyan ahalin gidan sarautar ingila yayin taron addu'o'in kirsimeti.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG