Wata sanarwa daga kamfanin dillancin labaran Fars a Iran, ta fadi cewar jiragen ruwan sintirin Iran, sun gudanar da aikin su ne, kamar yadda ya kamata, kuma ba su shiga hanyar wasu jiragen ruwa daga wata kasa ba, musamman ma jiragen ruwan Burtaniyya.
A yau Alhamis, Burtaniya ta ce jiragen ruwan Iran sun yi kokarin toshe hanya da wani jirgin ruwan dakon man Burtaniya zai bi a yankin tekun Hormuz.
Wata sanarwar gwamnatin ta ce wasu jiragen Iran guda uku ne suka so toshe hanyar, amma suka juya da baya, bayan sun samu sakon kashedi daga wani jirgin ruwan yakin Burtaniya.
Dakarun Iran na musamman, sun musanta zargin da Burtaniya ta yi. Wata sanarwar da kamfanin dillancin labaran Fars a Iran, ta fadi cewa jiragen ruwan sintirin Iran sun gudanar da aikin su ne, kamar yadda ya kamata kuma ba su shiga hanyar wasu jiragen ruwa daga wata kasa ba, musamman ma jiragen ruwan Burtaniyyar.
A wani lamari na daban kuma, jiya laraba shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa, ba da dadewa ba zai kara sanya takunkumin karya tattalin arziki akan Iran, bayan haka Amurka ta zargi Iran din da yin barazanar nukiliya wadda ta sabawa yarjejeniyar kasa-da-kasa ta nukiliyar, da aka cimma a shekarar 2015 da zummar dakatar da shirin kera makaman nukiliyar Iran din.
Facebook Forum