Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burkina Faso Ta Dakatar Da Kafar Yada Labaran Faransa


FRANCE 24 - RFI -MEDIA
FRANCE 24 - RFI -MEDIA

Gwamnatin Burkina Faso dake karkashin mulkin soja ta dakatar da kafar yada labarai ta France 24 a kasar bayan da ta yada wata hirar da tayi da shugaban Al-Qaida na yankin arewacin Afika AQIM.

Dangantaka tsakanin Paris da Ougadougou ta tabarbare tun bayan juyin juya halin da aka yi a Burkina Faso a watan Oktoba. A watan janairun bana, Burkina Faso ta baiwa Faransa wata daya ta janye dakarunta bayan cikar wa’adin wata yarjejeniyyar soji wanda ya baiwa dakarun Faransa damar yakar ‘yan ta’adda, da ya hada da yin hakan a cikin kasar.

Tun farkon watan nan mai ci ne kafar labaran ta France 24 ta yada faifaiyin bidiyon wata hirar da tayi da Yezid Mebarek, wanda aka fi sani da Ubaydah Yusuf Al-Anabi, kuma aka yiwa lakabi da sarkin Al-Qaidaa daular musulunci na Maghreb.

Abu Ubaydah Yusuf al-Anabi
Abu Ubaydah Yusuf al-Anabi

Yin hira da shugaban AQIM ya nuna cewar “baya ga kasancewar France 24 a matsayin masu Magana da bakin kungiyar, mafi muni shine, ta basu kafar da zata hallasta ayyukan ta’addanci da yada kalaman batanci, a cewar ministan sadarwar Burkina Faso Jean-Emmanuel Ouedraogo a wata sanarwa.

Kafar labaran ta France 24 wacce gwamnatin Faransa ne take daukar nauyin ta ta ce wannan matakin duk zarge-zarge ne marasa tushe.

“Kafar ta France 24 ta fada a wata sanarwa,bata bashi dama ba kai tsaye inda ta kara da cewa, ta dai yi amfani da bayannan hirar da wani wakilin yayi a cikin dakin daukan shirye-shirye.

Da can baya a watan Dizamba, Ougadougou ta dakatar da kafar watsa labaran Faransa na Radiyo wato Radio France International wanda ita ma gwamnatin Faransa ke daukar nauyin ta bisa zargin abinda ta bayyana da yada labarum kanzon kurege da kuma baiwa ‘yan ta’addan Isalama murya.

XS
SM
MD
LG