Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar sojoji biyu tare da wasu da dama, lamarin da ya bayyana a matsayin "mai tashin hankali."
Buhari ya yi wadannan kalamai a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar wacce Muryar Amurka ta sami kwafi .
“Harin da matsoratan suka kai kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, da kan jami’an tsaro da lalata gidaje da shaguna, abu ne mai matukar zafi da kuma cin rai. Mu al’ummar kasar baki daya na jimami da al’ummar Kagoro, inda aka kai hare-haren da sojoji da suka rasa jajirtattun ‘yan uwansu,” in ji Shugaban.
Shugaba Buhari ya ce yana matukar bibiyar matakan da gwamnatin jihar Kaduna da jami’an tsaro ke dauka domin zakulo maharan da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.
Ya kuma yi gargadin a guji ramuwar gayya da ka iya haifar da tashin hankali.