Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yaba Da Goyon Bayan Da Amurka Ta Nuna wa Najeriya Kan Zaben Okonjo-Iweala


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi lale marhabin da goyon bayan da Amurka ta nuna wa Dr. Ngozi Okonjo Iweala wacce ake fatan za a zaba a matsayin sabuwar shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya WTO.

“Mun yi matukar lale marhabin da wannan mataki da gwamnatin Amurka ta dauka, na janye shinge na karshe da zai ba Dr Okonjo-Iweala damar zama mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko da za ta jagoranci kungiyar.” Wata sanarwa sanye da sa hannun hadimin Shugaba Buhari Garba Shehu ta ce.

Sanarwar ta kara da cewa, “Najeriya da daukacin nahiyar Afirka na farin cikin wannan sabon matsayi da Amurka ta dauka, wanda ya bude wani babi na dangantaka tsakanin nahiyarmu da Amurka, karkashin gwamnatin Biden.”

“A yau, muna kallon Amurka a matsayin wacce take marawa Najeriya da Afrika baya ta hanyar aminta da ‘yar kasarmu da muke karramawa wacce za ta jagoranci WTO.”

Sanarwar ta kara da cewa, Najeriya na muradin ganin ta yi aiki kafada da kafada da sabuwar gwamnatin Amurka kan wannan batu da dukkan sauran batutuwa da kasashen biyu suke da manufofi iri daya.

Tsohuwar gwammnatin Trump ta ki mince da zabin Okonjo-Iweala a baya, duk da cewa kasashen da ke mambobin a kungiyar sun zabe ta.

Ita dai tsohuwar gwamnatin ta Trump tana goyon bayan ‘yar kasar Korea ta Kudu ne.

Amma a ranar Juma’a, ‘yar takarar ta Korea ta Kudu ta janye daga neman mukamin, abin da ya karawa Okonjo-Iweala damar samun wannan mukami.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG