Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Jajanta wa Italiya, Iran Kan Karuwar Coronavirus a Kasashensu


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Jiya lahadi, Shugaba Buhari na Najeriya ya aika wa shugabbanin kasashen Iran da Korea ta Kudu, da frai ministan Italiya sakonnin jaje, inda ya nuna matukar juyayi kan karuwar yaduwar cutar Coronavirus a kasashensu.

A cikin sakon, shugaba Buhari ya ce gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da taimaka wa kasashen waje, wajen tabbatar da ta dakile yaduwar cutar.

Shugaban ya kuma umarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da nuna soyayya da kauna ga dukannin ‘yan kasashen waje da ke zaune a Najeriya.

A cewarsa, “Babu dalilin tada hankali. Italiya da Korea ta Kudu da kuma Iran zasu ci gaba da zama kawayen Najeriya a cikin lokutan wuya da na farin ciki.”

A yayin da ya ci gaba da yaba wa kasashen kan kokarin da suke yi don dakile cutar, ya bayyana matukar kwarin gwiwa cewa, “da goyon bayan hukumar lafiya ta duniya (WHO), da sauran kungiyoyin duniya da ke aiki tare da juna domin dakile wannan kwayar cutar, cikin lokaci kadan duniya za ta ga karshen wannan cutar.”

Shugaban ya jaddada cewa, “a yanzu, babu alamun cutar a kasarmu. Mutum daya ne kawai ke dauke da ita, wanda ya zo da ita daga kasashen waje.”

A wani yunkuri na cika alkawarin da yayi wa hukumomin lafiyar Najeriya na basu duk abin da suke bukata domin tabbatar cewa cutar bata shigo kasar ba, ma’aikatar kudi da kasafi da kuma tsare-tsare, ta tabbatar da mika kudaden da suka kai milliyan 984 a yanzu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG