Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Na Jimamin Rasuwar Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Madeleine Albright


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga shugaban Amurka Joe Biden, da iyalan Albright, da kuma jami'an diflomasiyyar duniya, bisa rasuwar mace ta farko da ta rike mukamin sakatariyar harkokin wajen Amurka, Madeleine Albright.

Shugaban ya tuna da ganawarsa da jami'ar diflomasiyyar kasa da kasa a Washington a shekarar 2015, yana mai tunawa yadda ya ji dadin ganawar na hazakar mace da ta yi fice cikin mukaman da aka fi sanin maza ne ki rike da su.

"Ta taimaka wajen tsara da tafiyar da manufofin kasashen yammacin Turai bayan yakin basasa. Za a yi kewar ta sosai,” in ji Shugaba Buhari cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar a ranar Alhamis.

Yayin da yake yin waiwaye kan ayyukan da ta yi a matsayinta na mace ta farko da kasance jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya a zamanin mulkin Bill Clinton, sannan daga baya ta zama Sakatariyar harkokin waje, Shugaba Buhari, Albright ta dabbaka kare hakkokin bil Adama da tsarin Dimokradiyya a sassan duniya.

Buhari ya kara da cewa, Albright ta kuma taimaka wajen samar da kudade ga masu burin tsaya takarar shugaban kasa, sannan ta kasance daya daga cikin shugabannin kwamitin kasa da kasa mai tabbatar da adalci, tsaro da shugabanci na gari a duniya, inda ta yi aiki tare da Farfesa Ibrahim Gambari na Najeriya.

Shugaba Buhari ya kuma jinjinawa Albright don iri shawarwari da ta rika baiwa matasa jami’an diflomasiyya, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG