Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Britaniya Ta Rufe Ofishin Jakadancin Iran A Ingila


Masu zanga zanga a ofishin jakadancin Britaniya dake birnin Tehran nan Iran.
Masu zanga zanga a ofishin jakadancin Britaniya dake birnin Tehran nan Iran.

Britaniya ta bada umarnin rufe ofishin jakadancin Iran a London, ita kuma ta rufe ofishin jakadancin ta a Tehran.

Britaniya ta bada umarnin rufe ofishin jakadancin Iran a London, ita kuma ta rufe ofishin jakadancin ta a Tehran, sakamakon harin da gungun mutane suka kai wa ofishin jakadancin ta dake helkwatar Farisa a jiya talata.

Sakataren harkokin wajen Ingila William Hague ne ya bada sanarwar tsaida wan nan shawara a zaman majalisa yau laraba.

Yace an baiwa ma’aikatan ofishin jakadancin Iran sao’I 48 da su bar Ingila.

William Haque yaci gaba da cewa “idan wata kasa ta hana mu aiki a cikin kasarta, kada su yi tsammanin su zasu sami sukunin aiki a kasarmu.

Haque ya kara da cewa matakin nan da Ingila ta dauka ba yana nufin ta yanke huldar difilomasiyya da Iran bane. Sai dai kamar yadda yace, hakan ya rage hulda da Iran zuwa wani matsayi mafi kankanci ta fuskar difilomasiyya.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG