Tuni har an fara shirye-shiryen zaben wanda ake sa ran gudanar da shi a watan Yunin wannan shekara.
Rabon dai da a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar ta Borno tun a shekarar 2008, saboda tabarbarewar tsaro.
Hakan na nufin shekara 12 kenan, ake tafiyar da al’amuran kananan hukumomi ba tare da zababbun shugabanni ba.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Borno, Alhaji Abdul Usman, ya sheda wa wakilinmu Haruna Dauda Biu cewa, za a gudanar da zabukan ne a mazabu 5,071.
Ya kuma bayyana masa cewa za su yi amfani da rajistar da hukumar zabe mai zaman kanta ta yi wa al’umar jihar, sa’anan ba za su yi amfani da na’urar tantance masu zabe da ake kira “Card Reader” ba.
“Duk wanda ya zauna a Borno a shekarun baya zai san cewa an samu karuwar zaman lafiya,” a cewar Usman.
Idan dai an gudanar da wadannan zabukan, wannan zai zamanto karo na uku kenan da aka yi zaben kananan hukumomi karkashin hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar.
Saurari cikakken rahoton a sauti daga bakin wakilinmu Haruna Dauda Biu.
Facebook Forum