Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Nuna Ragowar ‘Yan Matan Chibok


'Yan kungiyar "Bring Back Our Girls" masu fafutukar neman a sako 'yan matan Chibok, a wani gangami da suka yi a watan Afrilun bara a jihar Legas
'Yan kungiyar "Bring Back Our Girls" masu fafutukar neman a sako 'yan matan Chibok, a wani gangami da suka yi a watan Afrilun bara a jihar Legas

An ji duriyar wasu daga cikin ragowar 'yan matan makarantar Chibok da kungiyar Boko take garkuwa da su tun a shekarar 2014 bayan da kungiyar ta saki wani sabon bidiyo.

Kungiyar Boko Haram mai ta da kayar baya a Najeriya da kasashe makwabta, ta fitar da wani sabon bidiyo da ke nuna wasu daga cikin ragowar ‘yan matan Chibok da ke hannunta.

Bidiyon ya nuna wasu ‘yan mata a zaune sanye da hijbai masu luanin shudi.

Daga cikin ‘yan matan wadanda kididdiga ta nuna za su kai su 12, akwai wata sanye da farin nikabi wacce ta yi magana a madadinsu.

Bidiyon ya nuna daya daga cikin 'yan matan tana kira ga iyayensu da ke Najeriya da su “tuba.”

A cikin bidiyon har ila yau, jagorar 'yan matan ta nuna cewa ba za su koma gida ba.

Wannan shi ne bidiyo na biyu cikin kwanaki 15 da kungiyar ta fitar a wannan shekara kamar yadda jaridun yanar gizon Najeriya da dama suka wallafa.

A farkon shekaran nan kungiyar ta fitar da wani bidiyo inda ta dauki alhakin kai wasu hare-hare.

A baya, dakarun Najeriya sun yi nasarar kubutar da daya daga cikin 'yan matan mai suna Salomi Pogu a wani kauye da ke Borno.

Gabanin haka, a watan Mayun bara, kungiyar ta saki sama da 'yan matan 80 bayan wata yarjejeniya da aka yi da hukumomin Najeriya.

Rikicin Boko Haram wanda ya samo asali tun daga 2009 daga jihar Borno, ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 20,000 ya kuma yadu har zuwa wasu kasashe makwabta kamar su Kamaru da Chadi da Nijar.

Dakarun Najeriya sun yi nasarar kwantar da wutar rikicin daga tsakiyar shekarar 2015, lamarin da ya ba da damar kwato yankunan kamar Gwoza da suka fada hannun mayakan kungiyar.

Koda yake a ‘yan watannin baya-bayan nan kungiyar ta kai wasu daidaikun hare-hare da suka kai ga rasa rayuka da dama.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG