Duk da yarjajjeniyar da ake cewa gwamnatin Najeriya ta cimma da mayakan Boko Haram, wadda aka ce ita ce ma ta yi sanadin sakin wasu ‘yan matan Chibok 21, ‘yan Boko Haram din ba su daina kai hare-hare ba cikin ‘yan kwanakin nan. Kodayake gwamnatin Najeriya ta karyata labarin cimma yarjajjeniyar da kuma sakin wasu jagororin Boko Haram. Haka zalika, yanzu akwai bangarori biyu a kungiyar ta Boko Haram.
Daraktan yada labarai na hedikwatar sojin Najeriya, Janar Rabe Abubakar, ya gaya ma wakilinmu Hassan Maina Kaina cewa sam ba a saki wasu kwamandojin Boko Haram don a sako ‘yan matan Chibok ba. Ya ce sasantawar da aka yi da kungiyar Boko Haram ma wannan aikin wasu kungiyoyi ne da ‘yan siyasa. Don haka, ya ce babu wata alaka tsakanin batun sakin jagororin ‘yan Boko Haram din da sabbin hare-haren da su ke kaiwa.
Haka zalika, a wata sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta bayar, kakakinta, Kanar Sani Usman Kukasheka ya ce a ranar Jumma’a ‘yan Boko Haram sun kai hari kan Bataliya ta 119 da ke Malamfatori, inda su ka hallaka sojojin Najeriya hudu, yayin da kuma sojojin su ka kashe ‘yan Boko Haram 14. Manjo Muhammad Abu Ali, wani kwarzon yaki da Boko Haram da aka kara masa girma zuwa matakin Laftana Kanar kwanan nan, na daya daga cikin sojojin Najeriya da su ka rasa rayukansu kwanan nan a hare-haren na Boko haram.
Ga wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton: