Kungiyar nan ta masu zazzafan ra'ayin addini masu da'awar Islama, da aka fi sani da sunan Boko Haram ta dauki alhakin kai harin nan da akai ranar lahadi kan jerin gwanon masu jana'iza a arewacin kasar.
A lokacin harin ne aka kashe fiyeda mutane ashirin ciki har da wasu fitattun 'yan siyasa biyu.
'Yan Sanda sun dora laifin harin da aka kai tun farko kan kauyukan yankin kan Fulani makiyaya, da kuma hari na biyu da aka kai kan masu jerin gwanon jana'izar wadan da aka kashe a farmakin da aka kai kan kauyukan.
A cikin wani sakon email da kungiyar ta aikewa 'yan jarida, Boko Haram ta dauki alhakin kai hare heren da aka kai a jihar Flaton, suna masu cewa "zamu ci gaba da farautar jami'an gwamnati ko ina suke."