BOKO HARAM—Tawayen da ‘yan Boko Haram ke yi a Nijeriya ya dada tsanani da kuma fadada ne 2014. A watan Afirilu wadannan masu tsattsauran ra’ayin sun sace ‘yan mata dalibai sama da 300 daga garin Chibok, su ka kuma shiga kwace yankuna su na maida su karkashin ikonsu a jihohin Borno da Yobe da Adamawa. A cikin watannin Mayu da Yunin 2014, ma’aikacin Sashen Hausa Ibrahim Alfa Ahmed, ya shafe watanni uku ya na ta kai-komo tsakanin wadannan jihohi na arewa maso gabashin Nijeriya masu cike da hadari, inda ya yi ta turo da wasu manyan labarai da dama, ciki har da na harin da aka kai kan wani sansanin soji da ke Buni Yadi da ke jihar Borno da kuma mamayarsa; da wani harin kuma da aka kai kasuwar Mubi da ke jihar Adamawa da kuma na hari a garin Madagali da shi ma ke jihar ta Adamawa, ‘yan sa’o’i kadan bayan ya bar garin. Wani sojin da ke barikin soji na Bama, wanda a yanzu haka ke karkashin ikon Boko Haram, ya bayar da bayani da kuma hoton bidiyo na yadda sojoji kan yi kashe-kashe ba bisa ka’ida ba; kuma wani dan sandan bangaren yaki da ta’addanci a Maiduguri ya bayar da bayani kan yadda har sai sun bai wa manyan jami’an soji na-goro kafin a ba su isassun albarusai yayin da za su sintiri.
SIYASA – A daidai lokacin da Nijeriya ke shirin gudanar da babban zaben 2015, manyan jam’iyyun siyasa sun gudanar da zabukan fitar da ‘yan takara, wani zubin cikin yanayi na rikici, don zabar wadanda za su tsaya masu takarar. Jam’iyyar da ke mulkin Nijeriya ta yanke shawarar tsai da Shugaba Goodluck Jonathan ba tare da zabe ba, a yayin da kuma bangaren adawar ya gudanar da zaben fidda dan takara tsaknin mutane biyar, inda tsohon Shugaban mulkin soji Muhammadu Buhari, ya zama dan takararta. Sashen Hausa ya ba da labaran kowace jam’iyya.
EBOLA – Bayan da wani dan asalin Liberiya mai dauke da cutar Ebola ya tafi Nijeriya, sai cutar ta fara bazuwa cikin kasar, abin da ya haddasa fargaba da kuma zaburowar hukumomin kasar wajen hana bazuwar cutar daga inda aka dauki dan Liberiya din kafin ya mutu. Hukumomin lafiya a fadin duniya sun jinjina ma Nijeriya saboda tsaidawa da kuma dakile bazuwar cutar ta Ebola a kasar. Sashen Hausa ya yi jagoranci wajen yada labaran matsalolin Ebolar a Nijeriya.