Binciken sanin ra’ayin jama’a bayan kada kuri’a na nuna cewa Francois Hollande ya yi galaba a kan Nicolas Sarkozy a zaben fidda gwanin da aka yi a Lahadin nan a kasar Faransa.
Hasashen da aka yi ya kiyasta cewa Mr.Hollande ya lashe sama da kashi 50 cikin dari na kuri’un da aka kada, wanda hakan ya sa shi zama shugaban kasar Faransa dan jam’iyyar gurguzu na farko cikin shekaru kusan 20. Jim kadan bayan an rufe zabe, Mr.sarkozy ya kira abokin takarar ta shi, ya rungumi kaddara.
Alkaluman ma’aikatar harakokin cikin gidan kasar sun nuna cewa daga karfe ukun yamma kashi 72 cikin dari na ‘yan kasar da suka yi rajistar zabe har sun kada kuri’un su, wanda hakan ya nuna cewa a wannan karo mutane sun fita fiye da zagayen farkon da aka yi a watan jiya.
Mr.Hollande ya yi alkawarin gaggauta aiwatar da shirin da aka san jam’iyyar shi ta gurguzu da shi, wato shirin haraji da kasafin kudi wanda zai jibgawa attajirai haraji domin gwamnati ta samu karin kudin kasafi. Haka kuma ana kyautata cewa Waziriyar Jamus Angela Merkel zai fara ziyarta a kokarin neman sake tattaunawa akan matakan tsuke aljihun gwamnatin da Tarayyar Turai ta kwakubawa kasar.