Bakin hauren da Birtaniya ta taso keyarsu zuwa Najeriya ta yi zargin cewa suna kasarta ne ba tare da samun takardun zama kasar ba. Yawan mutanen ya kai dari biyar.
Wadanda aka dawo dasu wasunsu suna gararamba a harabar filin saukan jiragen sama na kasa da kasa dake Legas saboda basu san inda zasu je ba.
Cikin wadanda aka dawo dasu akwai wadanda ba 'yan Najeriya ba ne. Akwai 'yan kasar Barbedus a cikinsu.
Muryar Amurka ta zanta da wasu cikinsu. Wani ya ce shi ba dan Najeriya ba ne. Shi dan asalin kasar Barbedus ne kuma kodayake shi ba dan Birtaniya ba ne amma ya kwashe shekaru 15 yana zaune cikin kasar. Yace shi babu wata kasa da ya sani idan ba Birtaniya ba.
Wasu bakin hauren da aka dawo dasu sun zargi jami'an ofishin jakadancin Najeriya da jami'an shige da fice dake Legas da sanya hannu a takardar karbar su duk da cewa su ba 'yan Najeriya ba ne. Sun kira shugaban kasa Muhammad Buhari da ya sa baki.
Har wa yau sun kira shugaban kasa ya yi magana da jami'an Najeriya dake ofishin jakadancinta a Birtaniya da su daina cin hanci domin suna zubar da mutuncin kasar ne.
Su dai bakin hauren tuni suka bazu cikin garin Legas lamarin da ake gani yana iya zama barazana ga harkar tsaro ga kasar.
Ga karin bayani.