Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bin Koyarwar Addinai Shine Kadai Hanyar Samu Shuwagabannai Adilai


Matasa
Matasa

Wani shahararen malamin adini, Shiek Tijjani Bala Kalarawi, ya yi kira ga jama’a musamman matasa da su bi dokokin hukumar zabe, kuma su bi koyarwar addinin Islama, don neman samun tsira.

Yace, idan har al’umah na neman nasara a duk abubuwan da suke yi, to su kasance masu yima shuwagabannin su adalci da kuma addu’a, kuma su sani dacewar sai sunyi ma kansu adalci kamin su ga shugabanin su sunyi musu adalci.

Cikin karin bayanin shi, yayi kira ga mutane da su yi kokari a lokutan zabe su bi doka kuma kada su bar hakokinsu na addini don zabe. Domin kowanne yana da huruminsa na daban. Bugu da kari, al'umah su sani zaben nagari shine mafita ga kasar baki daya don haka shiga bangar siyasa ko karban kudi don zaben wasu bashine abu da yakamata a ce utane sun sakansu a ciki ba, don wannan karon siyasar wannan zamani ta wuce haka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG