Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Berlusconi Ya Kai Ziyarar Bazata


Silvio Berlusconi -Tshon Firai Ministan Italy
Silvio Berlusconi -Tshon Firai Ministan Italy

Tsohon Firai ministan Italiya Silvio Berlusconi yayi wata ziyarar bazata a wata mujami’a a Napoli a jiya Asabar, wuni guda kafin babban zaben yan majalisar dokoki da Italiyawa zasu yi.

An haramtawa 'yan siyasa yakin neman zabe a ranar Asabar, amma ziyarar da Berlusconi ya kai a mujami’ar Sansevero ya janyo dimbin manema labarai da magoya baya. Berlusconi mai shekaru 81 a duniya ya fadawa manema labarai cewa shi da budurwarsa mai shekaru 30 sun ziyarci mujami’ar ne a kan yawon bude ido. Yace wannan mujami’a tana cikin abubuwa da kasar ta gada da babu wata kasa a duniya dake da irinta.

Berlusconi da yayi mulkin wa’adi hudu a matsayin Firayi Minista, ba zai yi tsayawa takara a zaben na ranar Lahadi ba, saboda laifin damfarar haraji da aka sameshi dashi a shekarar 2013, amma dai yana marawa jam’iya mai sassaucin ra’ayi ta Forza Italia baya kuma yana goyon bayan tsohon shugaban majalisar Tarayyara Turai Antonio Tajani ya zama Firayi Minista, idan jami’iyarsa ta samu kujeru masu yawa a majalisa.

Masu hasashe sun ce akwai yiwuwar sakamakon zaben ba zai ayyana kowace jamai’iya mai nasara ba, kuma hakan zai tilastawa jamai’iyyun su kafa gwamnatin hadin gwiwa, lamarin zai dauki makwanni babu tabbas wurin kafa gwamnati da zata yi aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG