Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bazamu Iya Magance Boko Haram ba a Sati Shida


Namadi Sambo
Namadi Sambo

Mataimakin shugaban Najeriya Alh. Namadina Sambo, ya bada tabbacin cewar hukumar zabe me zaman kanta, zata cigaba da bada katin zabe na dindindin, kuma yana me kyautata mata zaton zata gudanar da zabe me adalci. A bangaren tsaro kuma, yace suna sa ran jami’an tsaro zasu cigaba da yin kokarinsu don magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Wanda suna sa ran kamin nan da sati shida da za’a gudanar da zabe, sun magance kaso da dama, don a samu damar gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana. Yace kada mutane suyi kuskuren gane menene manufofinsu, ba suna nufi za’a kawar da boko haram bane kamin lokacin zabe, abun da suke nufi shine zasu yi kokari su samar da yanayi mai walwala ga ‘yan Najeriya don su samu damar kada kuri’a batare da barazanar ‘yan ta’adda ba.

Ya kara da cewar shawo kan wannan matsalar ba wai abune kawai na Najeriya ba, abune da ya shafi sauran kasashe azo a hada hannu don kawo karshen wannan abun.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG