Kamar yadda muka saba jin ra'ayoyin samari daban daban akan wasu lamurra na rayuwa da zamantakwa, a wannan makon mun nemi jin ra'ayoyin samari da 'yan mata ne akan dalilan da ke sa matasa auren mata fiye da guda baya ga umurnin addini.
Daga cikin matasan da muka sami jin tabakin su, Malam Aliyu Suwidl ya bayyana ra'ayin sa kamar haka, "akwai dalilai da dama da ke sa matasa ko samari auren mace fiye da guda baya ga umurnin addini, na farko shine rashun jituwa ko mutunta namiji daga matar sa, ko kuma rashin jituwa da dangin sa.
Ya kara da cewa kodashike wasu samarin suna da halin gane gane, wato duk sa'adda suka wata mace sai hankalin su ya koma kanta, kuma akwai akwai yaudara. Wannan na nufin kasancewa namiji ya auri matar da baya so".
Da muka karkata akalar shirin, Malam Hassan Awal Muhammad cewa yayi rashin iya kwalliya da dafa abinci da sauran abubuwa makamantan su kadai sun isa su sa namiji ya ji mace ta fitar masa a rai.
Ga cikakkiyar hirar.