Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bauchi: An Sami Karuwar Masu Aikata Fyade


Wasu da 'yan sanda suka kama da laifin yin fyade.
Wasu da 'yan sanda suka kama da laifin yin fyade.

A jihar Bauchi hukumar ‘yan Sanda ta bayyana cewa an samu karuwar masu aikata fyade daga farkon shekarar nan, wanda yakai har an kama mutane 25.

kwamishinan yan sandan jihar Bauchi Garba Baba Umar, shine ya shaida hakan a taron manema labarai. Inda yace rundunar yan Sandan tayi nasarar kama matasa yan sara suka kimanin 150.

A cewar kwamishinan yawaitar masu aikata fyade a jihar Bauchi ya kazanta ya zama annoba, inda ya zama zuwan dare musamman a ‘kauyuka da bayan gari, wasu lokuta kuma akan samu ‘yan uwa na jini ne ke aikata wannan ta’asa.

Bayan matsalar fyade kuma, sai kuma matasa ‘yan sara-suka da ke addabar mutane a garin Bauchi, wanda yanzu haka rundunar ‘yan sanda ta cakfe matasan har 150 cikin har da wani da ya shahara a fannin sara-suka mai suna Hakori.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG