Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Duniya Zai Taimakawa Jihohi Uku Su Samarda Ruwan Sha


Muhammad Rilwan Sulaiman, Sarkin Bauchi
Muhammad Rilwan Sulaiman, Sarkin Bauchi

Wata tawagar Bankin Duniya tana Bauchi saboda ta tabbatar jihar ta yi anfani da kaso goma cikin dari na kudin da take bukata domin inganta ruwan sha kana bankin ya bada kaso casa'in

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi Injiniya Nuhu Gidado ne ya tarbi tawagar a gidan gwamnatin jihar.

Ya bayyana makasudin ziyarar tawagar zuwa jihar. Tawagar ta Bankin duniya ta isa jihar ne saboda tallafin da bankin zai bayar akan samarda ruwan sha. Jhiar na cikin jihohi uku da bankin zai taimakawa domin su samarda ruwan sha. Sauran jihohin kuwa sun hada da Ekiti da Rivers.

Bankin ya ba jihohin tallafin dalar Amurka 65 kowanensu to saidai bankin ya gindiya masu wasu sharruda. Jihar Bauchi ya kamata ta bada kashi goma daga cikin dari kafin ta fara karbar kudi daga bankin duniya. Jihar yanzu ta bada kashi goman dalili ke nan da ya sa tawagar bankin ta zo ta ga shirye-shiryen da aka yi.Jihar ta yi masu kukan cewa sun cika ka'ida saboda haka a sakan masu kudi su cigaba da aikin madatsar ruwan Gubi ko Gubi Dam.

Tun shekarar 1992 aka gina Gubi Dam amma ba'a samu gwamnatin da ta zauna ta ga an fadada dam din ba. An bar dam din yanzu koda an fadadata dari bisa dari ba zata ishi mutanen Bauchi ba.

Hassan Madu Kida jami'in bankin duniya kan samarda ruwan sha ya shaidawa manema labarai abubuwan da shirin samarda ruwan ya kunsa. Yace sun amince da bada kudin ga jihar domin ta fadada hanyoyin samarda ruwan sha a cikin gari da karkara. Sun samarda kudi dalar Amurka 65 da zasu ba Bauchi.Zasu horas da ma'aikatan ma'aikatar ruwan jihar.

Jami'in bankin yace yarjejeniyar bada bashin tana tsakanin gwamnatin Najeriya ce da Bankin Duniya kana ita gwamnatin Najeriya ta shiga yarjejeniya da gwamnatin Bauchi. Bankin ba kuma zai bada kudin gaba daya ba. Ana aiki ana bada kudin kadan kadan. Bankin sai ya tabbatar ana gudanar da aikin kamar yadda ya tsara kafin ya bada kudi.

Bankin ya gamsu da abun da ya gani saboda jihar ta bada dalar Amurka miliyan shida da digo shida.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG