Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangaren Ali Modu Sheriff Na Ganin Dattawan PDP Muzurai Ne


Sanata Ali Modu Sheriff wanda ake ja da shi a PDP
Sanata Ali Modu Sheriff wanda ake ja da shi a PDP

Farfasa Jerry Gana na kwamitin amintattun PDP yace dole ne a samu rarrabuwan ra'ayoyi amma duk inda aka ce akwai dattawa alamura basa baci, gyaruwa su keyi.

Farfasa Jerry Gana ya yi magana ne a Abuja a lokacin da ya je domin sasantawa da Sanata Ali Modu Sheriff wanda yake shugabancin wani bangaren jam'iyyar.

To saidai kwamitin amintattun ya dauki matsayin marawa Ahmed Makarfi baya domin ya karbi shugabancin jam'iyyar. Amma yunkurin bai yi nasara ba domin Ali Modu Sheriff ya cigaba da bin shari'arsa a kotu dangane da shugabancin jam'iyyar.

Yayinda da Sanata Sheriff yake Abuja shi kuwa Makarfi yana Fatakwal wajen zaben sabbin shugabanni.

Mai masaukin baki gwamnan Nwike na jihar Rivers ya cigaba da taron yana cewa suna da hukumci daga kotun tarayya dake Fatakwal wanda ya amince da taron sabanin umurnin da kotun Abuja ya bayar na dakatar da taron.

Sanata Ali Modu Sheriff ya kushewa taron Fatakwal din yana cewa hatta kwamitin sulhun da aka turo masa abokan hamayyarsa ne.

Inuwa Bwala kakakin Modu Sheriff yace kwamitin neman sulhu na muzuru ne, wato mutanen dake cikin kwamitin din muzurai ne saboda duk suna bayan Ahmed Makarfi. Yace basu bi yarjejeniyar da aka yi ba. Wani abu daban suka je suna yi.

Yayinda da wasu manyan ke neman shugabancin jam'iyyar shi kuwa Ali Modu Sherif cewa yake yana da hurumin cigaba da zama shugabanta har zuwa shekarar 2018.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG