Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bama Bamai Sun Fashe a Wata Kasuwa a Pakistan


Fashewar Bama Bamai A Pakistan Parachinar.
Fashewar Bama Bamai A Pakistan Parachinar.

Fashe-fashen sun faru ne a babbar kasuwar garin Parachinar, wanda shine gari mafi girma a lardin Kurram dake kusa da inda Pakistan tayi kan iyaka da Afghanistan.

Wasu fashe-fashen bama-bamai guda biyu da suka faru, daya bayan daya a arewa-maso-yammacin kasar Pakistan, sun janyo mutuwar mutane akalla 25, da raunana wasu fiye da 100.

Fashe-fashen sun faru ne a babbar kasuwar garin Parachinar, wanda shine gari mafi girma a lardin Kurram dake kusa da inda Pakistan tayi kan iyaka da Afghanistan.

Sajid Turi, wani dan majalisar dokoki daga yankin, ya gaya wa kafofin watsa labarai cewa bama-baman sun tashi ne a daidai lokacinda mutane ke cikin hidimomin shirin komawa gidajensu daga wajen sana’oinsu.

Dan majalisar yace yana sa ran cewa yawan wadanda zasu rasa rayukkansu a al’amarin zai karu, da yake akwai mutane akalla 30 da aka kawo, wadanda suka ji rauni, wadanda kuma ke cikin abinda ya kira “mawuyacin hali mai tsanani.”

Akwai alamar cewa an auna ‘yansanda ne a cikin hare-haren don akalla bakwai daga cikin wadanda aka kashen, duk ‘yansandan ne.

Tuni dai wata kungiya mai suna Jama’atul Ahrar, wadda reshen kungiyar Taliban ce, ta dauki alhakin kai farmakin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG