.Wannan shine karon farko da ake samun irin wannan tashin hankalin tun bayanda aka soma aiwatarda yarjejeniyar sulhu a makon jiya, a cewar kafofin watsa labaran kasar.
Wata kungiyar kare hakkin mutanen Syria da mazauninta yake a Ingila mai suna “Observatory” ma cewa tayi mutanen da suka hallaka sun kai 14.
Daman tun ma kafin wannan ta faru, yarjejeniyar tsagaita fadan ta soma tangal-tangal bayanda sojan gwamnati suka tsananta hare-haren da suke kaiwa a kusa da Damascus, babban birnin kasar, yayinda su kuma mayakan ‘yantawaye suka fara bayyana anniyarsu ta janyewa daga taron karfafa sulhun da ake shirin yi a cikin watan nan.
Rasha, Turkiyya da Iran ne ke jagorancin shirya wannan taron sulhun da ake son yi a kasar Kazakhstan.