Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam da Ya Tarwatse A Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar


A yayinda aka soma sake jiki a Maiduguri sai gashi yau da safe wani bam ya tashi a wata tashar mota inda ya hallaka mutane biyar tare da jikata wasu.

Da misalin karfe takwas na safiyar yau ne wani bam ya tashi cikin garin Maiduguri a tashar motar Munadare da yayi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da jikata wasu da dama.

Rahoton da kakain 'yansanda jihar Borno ya fitar DSP Victor Isoko ya tabbatar da mutuwar mutane biyar wasu biyar kuma suka samu raunuka. Duk mutanen biyar da suka mutu suna cikin wata mota ce kirar Gulf. Mata hudu da direban motar suka halaka.

Wannan sabon hari shi ne baya bayan nan tun wani harin da aka kai kofar sakatariyar jihar a cikin Maidugurin wanda ya hallaka jami'an 'yansanda biyu.

Watanni hudu ke nan da babban hamsan sojoji ya bude hanyar wadda ta tashi daga Maiduguri zuwa garin Gamboru inda aka samu tashin bam din yau.

Saidai rahotanni daga asibitin koyaswa na Jami'ar Maidugur ya ce mutane bakwai ne suka halaka yayinda 15 suka jikata.

Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da mutuwar mutane biyar a tashar yayinda ban din ya tashi.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG