Anyi zargin cewa kimanin bakin haure 500 ne hukumomin shige da fice na kasar Ingila suka dawo dasu Najeriya, A yayinda wasunsu sukace su ba yan Najeriya bane.
A hirar da Babangida Jibril ya yi da wasu daga cikin bakin hauren a filin jirgin kasa da kasa da ke birnin Lagos, daya ya bayyana cewa shi dan kasar Babedors ne kuma shekarun sa goma sha biyar a kasar ta bitaniya babu kuma inda ya sani in ba kasar ba.
Bakin hauren sun koka da cewa wasu daga cikin ma'aikatan shigi da fice da kuma ma'aikatan filin jirgin ne suka sa hannun amsar su a Najeriya duk da cewa su ba 'yan kasar bane, sun kuma yi kira ga shugaba muhammadu Buhari da ya sa baki a lamarin, kuma su daina karbar cin hanci domin kuwa suna zubar da mutuncin kasar.
A halin da ake ciki dai yanzu da yawansu sun shiga gari lamarin da wasu ke ganin cewa barazanar tsaro ne ga Najeriyar musamman yadda aka barsu suka shiga gari ba tare da an tantance su ba.
.Ga rahoton Babangida jibril.