A jamhuriyar Nijar ce-ce ku-ce ya barke bayan da wata jarida mai zaman kanta ta wallafa wasu bayanan dake nunin da cewa gwamnatin kasar ta sayarwa wani kamfanin kasar Rasha, ton dubu biyar 5000 na Uranium a shekarar 2011 wadanda kuma aka biya kudinsu a asirce a wani bankin Dubai, koda yake gwamnatin ta musanta wannan zargi.
A bayanan da ta bayar Jaridar Lukure, wace ita ta bankado wanna labara ta wallafa wata takarda dake nunin an yiwa gwamnatin Nijar Zubin miliyan dari uku da tasa’in na dala Amurka, ($390) a wani asusun bakin dake Dubai, a shekarar 2011, sakamakon cinikin ton biyar (5000) na Uranium, tsakanin wani kamfanin kasar Rasha da darektan fadar shugaban kasa na wancan lokaci minsitan kudi a yau Hashimi Masahudu.
Minista Hashimi Masahudu, yace abinda ya faru a zahiri shine kasar Nijar ta yiwa kamfanin Areva, shugabanci mai kamar dillanci domin cike ka’idojin wani cinikin na ton dubu hudu (4000) na Uranium, da kamfanin na Faransa, ya saidawa wasu abokan huldansa wadanda aka zuba a wani bankin Dubai, dalillin Kenan da kamfanin na Areva, ya baiwa Nijar miliyan dari takwas na Saifa, a matsayin la’ada wadanda fadar shugaban kasa tayi amfanin dasu domin sayan motocin rundunar tsaron lafiyar shugaban kasa saboda haka zargin yin rubda cikin da ko sayarda Uranium a boye ba gaskiya bane in ji ministan.
Tuni dai shuwagabanin kungiyoyin fafutuka irin su Hamidu Sidi Fodi, na ONDDCV, suka yiwa wannan batu cha suna masu nuna rashin gamsuwa da bayanan na ministan kudi.
Hamidu Sidi, yace a bar shara’a tayi aikinta domin talakawa na bukata sun san gaskiyar alamarin.
A ci gaba da kokarin ganar da jama’a rashin sahihancin wannan labara, Ministan ta bakin na hannun damarsa Buobacar Sabo ya bukaci ‘yan kasar Nijar su gudanar da bincike da kansu.
Facebook Forum