Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Wani Shiri Na Hana Mata Tuki A Kano - Gwamnati


Kwamishinan yada labarai a Kano, Malam Muhammad Garba (Facebook/ Comrade Muhammad Garba)
Kwamishinan yada labarai a Kano, Malam Muhammad Garba (Facebook/ Comrade Muhammad Garba)

“Idan har akwai wani shiri makamancin hakan, gwamnati ba za ta tsaya tana wani taro a boye ba, dangane da wannan muhimmin batu da ya shafi rayuwar al’uma." 

Gwamnatin jihar Kano ta musanta rade-radin da ake ta yi cewa za a hana mata tuki a daukacin jihar, batun da ta ce labari ne na bogi.

Kwamishinan yada labarai a jihar Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis inda ya ce babu wani lokaci da gwamnatin jihar ta furta wani abu makamncin hakan.

“Wannan labari ba shi da tushe, dalilin kenan da ya sa aka daganta shi da wata majiya da ba za a iya tantancewa ba.” In ji Garba

Jama’a da dama a jihar ta Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun wayi gari da labarin a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna za a hana mata daga dukkan addinai tuki a jihar.

Amma a cewar kwamishinan yada labaran, “idan har akwai wani shiri makamancin hakan, gwamnati ba za ta tsaya tana wani taro a boye ba, dangane da wannan muhimmin batu da ya shafi rayuwar al’uma."

Ya kuma kara da cewa, kasar Saudiya ma da ta kwashe shekaru da dama da dokar da ta haramtawa mata yin tuki, ta dage dokar tun a shekarar 2018.

A cewar kwamishinan, wani abin mamaki kuma shi ne, dukkan malaman da aka dangantawa da lamarin tuni sun fito sun nesanta kansu da batun.

XS
SM
MD
LG