Sanata Emmanuel Bwacha yace 'yan Boko Haram na neman kafa sansaninsu a jihar ta Taraba sabili da saukar wani jirgi mai tashin ungulu yayi a wani kauye tare da mutanen da ba'a san ko su wanene ba. Batun ya kara tada hankulan mutane a yankin.
Yace a halin da kasar ke ciki idan ba'a shaidawa jami'an tsaro ba wani abu na iya tashi a ce an fada amma ba'a yi komi ba. Yace yakamata a fada kuma a bincika. Idan gaskiya ne to an taimaki jama'a. Idan kuma ba gaskiya ba ne hankali ya kwanta.
Ita gwamnatin jihar Taraba ta nuna bacin ranta game da furucin dan majalisar dattawan. Tace wani yunkuri ne na kawo fitina da wasu 'yan siyasa ke son yi. Ta bukaci al'ummar jihar da su kwantarda hankalinsu. Mukaddashin gwamnan yace dan majalisar ya fadi ra'ayinsa ne kawai. Yace an yi kame-kame kuma hukuma tana nan tana kan bincike. Sai a jira sakamakon binciken.
Sarkin Mumuye ya kira jama'a da su yi hakuri da juna kuma mahukunta su ba kowa hakinsa domin a samu zaman lafiya.
Ga karin bayani.