Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangladesh Ta Hana Aure Tsakanin 'Yan Kasar Da 'Yan Gudun Hijirar Rokhingya.


'Yan gudun hijira daga kabilar Rokhingya bayan sun isa Bangladesh.
'Yan gudun hijira daga kabilar Rokhingya bayan sun isa Bangladesh.

Hukumomin kasar suna neman ango Shaoib, da amaryarsa 'yar Rokhingya Rafiza,bayan d a suka daura aure wata guda da ya shige.

Duk da tashe tashen hankula da suka koro 'yan gudun hijirar Rohingya daga jahar Rakhine a Myanmar, la,mari da ya tilastawa 'yan kabilar su rabin Milyan tsallakawa ta kan iyakar kasar zuwa Bangladesh, hakan bai hana soyayya data kai ga aure tsakanin masu gudun hijira da Bangladesh ba.

Amma saboda dokoki masu tsanani da suka haramta auratayya tsakanin 'yan Bangladesh da 'yan gudun hijiran Rokhingya, ango da amaraya suna kan gudu.

Dan Bangladesh, Shaoib Hossein Jewel, dan shekaru 25,da amaryarsa Rafiza 'yar shekara 18 da haifuwa, suna zullewa hukumomin kasar, tun bayan da suka yi aure wata guda da ya shige. Kamar yadda 'Yansanda a garin Singair inda nan ne garin su ango.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG