Kamfanin sadarwar zamani na Twitter ya haramta amfani da kalaman batanci a shafukansa, musamman ga wasu mabiya addinai.
A jiya Talata kamfanin ya sanar da cewa ba zai amince da yadda mutane ke rubuce-rubuce na batanci ga mutane ba, ko kuma wasu kungiyoyi addinai su dinga yayata wasu kalamai da aka yi akan wasu ba.
Kamfanin dai ya fuskanci matsin lamba tare da wasu takwarorinsa kamfanonin sada zumuntar zamani da suka hada da Facebook, YouTube, da aka ce suna barin mutane na amfanin da kafofin na su wajen rubuta kalaman da ba su dace ba.
Kamfanin dai ya dau wannan matakin ne bayan wani binciken jin ra’ayin mutane akan tsarinsa na amfani da kalamai marasa dadi, inda dubban mutane suka amince da a sauya tsarin don kare hakokin wasu.
Ya kuma kara da cewar zai duba dokokinsa wajen ganin sauran mutane masu aika kalaman batanci ga wasu jinsin mutane sun magance shi.
Facebook Forum