Har yanzu dai ‘yan kasar Nijer maniyyata aikin Hajjin bana ba su san ranar da za su fara tashi ba, bayan da kamfanonin jigilar Mahajjata suka dage ranakun tashin da suka tsaida tun da farko.
Kafin wannan matsalar ta kunno kai dai da farin farko an ce da tun ranar takwas ga watan nan na Satumba Mahajjata ke fara tashi , a ci gaba da kwasar su zuwa kasar Saudiyya a ranakun tara da goma sha uku na watan Satumba.
Sai dai kuma duk kokarin da hukumomin kasar Nijer suka yi na neman yin rigakafin matsalolin dake tattare da shirya aikin Hajji, abun ya ci tura.
Kuma duk da wannan rashin tabbas yanzu haka maniyyata daga sassan kasar daban-daban sun cika Niamey babban birnin kasar makil, saboda galibi daga can aka saba kwasar su zuwa kasa mai tsarki.
Ga wakilin Sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou da ci gaban rahoton.