A daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke shirin ci gaba da tattaunawar sulhu da kungiyar Boko Haram a kasar Chadi Litinin din nan, dubban 'yan kasar ta Najeriya masu zaman gudun hijira a kasar Kamaru sun ce hankalin su bai kwanta da sulhun ba kuma sun koka da halin tagayyarar da suke ciki.
Yanzu haka akwai 'yan Najeriya kimanin dubu ishirin da biyar dake zaman gudun hijira a kasar Kamaru bayan hare-haren da 'yan Boko Haram suka yi ta kaiwa Gamboru N'gala.
Babban Editan Sashen Hausa Aliyu Mustaphan Sokoto ya tuntubi wasu daga cikin irin wadannan 'yan Najeriya masu gudun hijira a mazaunin su a kasar Kamaru.
Wanda ya fara magana shi ne Alhaji Mahamadu kamar yadda za ku ji: