Bayan ta rabu da dan wasanta shekaru biyu da suka wuce 2017, kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke kasar Spain, tana yunkurin dawo da tsohon dan wasanta Neymar, wanda ta sayar wa Paris-St German.
Barcelona ta ce za ta yi duk wani abin da za ta yi a wannan lokacin don ganin an cimma yarjejeniya kan dan wasan.
Neymar, mai shekaru 28 da haihuwa na samun takun-saka tsakaninsa da kulob din Paris-saint German, a kwanakin baya wanda ya kai shi kaurace wa filin atisaye na kungiyar kafin daga bisani aka sasanta.
A wannan lokacin an yi ta rade-radin dawowarsa tsohowar kungiyarsa ta Barcelona, amman abin ya cutura inda daga bisani ta sayo Antonio Griezmann, daga Atletico Madrid, da dan wasan tsakiya na Ajax Frenkie.
Wasu rahotanni daga Darektan wasannin Barcelona Leonardo, na nuni da cewar za su saye Neymar akan kudi fam miliyon £190, kwatankwacin dalar Amurka miliyon $246.
Sai dai a shekara 2017, Barcelona ta sayar da dan wasanta, dan kasar Brazil akan kudi Euro miliyon €222.
Facebook Forum