Kungiyar malaman Jami'o'i a Najeriya ASUU, ta ce ba gudu ba ja da baya dangane da yajin aikin da ta tsunduma a duk fadin kasar.
A makon da ya gabata, kungiyar malaman ta shiga yajin aiki na gargadi inda take kalubalantar kin biyan mambobinta albashinsu saboda sun ki yin rijista da tsarin biyan albashi na bai-daya, wato IPPIS.
Yayin wani taro da shugabannin kungiyar malaman jami’o’in ta ASUU suka yi jiya Talata a Yola, babban birnin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar, malaman sun ce suna nan kan fafutukarsu, wacce suka kwatanta a matsayin ta kawo sauyi a jami’o’in Najeriya.
‘’Dole ke sa wa mukan je yajin aiki, dubi yadda gwamnati kan yi shakulatin bangaro game da yarjejeniyar da aka yi a baya. Ai muna wannan fafutukar ne domin kawo gyara," a cewar Farfesa Augustine A. Ndaghu, wanda ya halarci taron.
Baya ga batun hakkokinsu da suke takaddama da gwamnati akai, yanzu haka wata matsalar ita ce ta balahirar Boko Haram da kuma garkuwa da jama’a, inda matsalolin kan shafi jami’o’i, musamman a shiyyar arewa maso gabas.
Saurari cikakken rahoton a sauti.