Tsohon mai baiwa tsohon shugaba Nigeria, Olusegun Obasanjo shawara a kan harakokin Noma Farfesa Ango Abdullahi yace matsalar Nigeria ba ta tsarin mulki kasa bace.
Farfesan yana maida martani ne akan kiran da shugabanni da gwamnati keyi na akai zuciya nesa game da tashe-tashen hankulan da kungiyar masu fafitikar kasar Biafra keyi.
Malamin na Jami’a yace asake duba al’amarin da idon basira domin ko ansha yiwa dokar kasa kwaskwarima amma har wa yau lamarin bai sake zani ba.
Yace muddin ba tsayawa akayi aka fadawa juna Gaskiya ba to har kullun za a koma ‘yar gidan jiya ne.
Shima da yake tofa albarkacin bakin sa game da wannan lamarin shugaban kungiyar nan da ake kira “Our Mumu Don Do”, Deji Yade Adeyanju yace sun goyi bayan bada belin Nnamdi Kanu ne da zummar cewa zaiyi fafitikar ganin an sama wa jama’ar yankin su ababen more rayuwa amma sai suka ga ya shiga wata sabga ta daban.
Ga Saleh Shehu Ashaka da karin bayani.
Facebook Forum