Shugaban kamfanin Google Sundar Pichai, ya fito ba tare da wata matsalaba daga taron shaida da yayi a gaban kwamitin Shari’a na Majalisar Dokoki Amurka.
Bayan da ya sha tambayoyi na kusan awanni hudu daga kwamitin shari’a na majalisar, akan zargin ko kamfanin na Google na shiga harkokin siyasa da nuna banbanci ko son kai.
An auna Pichai a matsayin mutun mai kamun kai da natsuwa da shiru-shiru, duk da wasu tambayoyi marasa ma’ana da yayi ta amsawa daga ‘yan majalisar.
Shi dai wannan zama ya samu halartar tsohon mai goyon bayan shugaban Amurka Trump, kuma dan adawar bakar fata, wanda ya kira kamfanin Google da suna “mugun kamfani, ko mai razanarwa.”
‘Yar majalisa Zoe Lofgren ta tambayi Pichai dalilin da yasa idan aka saka kalmar 'sha-sha-sha' 'Idiot' a turance, ake gani hotunan shugaba Amurka Donald Trump, ke fitowa? sannan dan majalisa Steve King ya tambaya shi me yasa wayar salula dinshi ta kamfanin Apple wadda ta kai kusan shekaru bakwai take bashi matsala, inda ya amsa mishi da cewa wannan wayar wani kamfani ne da ban.
Facebook Forum