WASHINGTON, DC: —
Bayan da ta kwashe shekaru sama da 30 rabonta da daukar kofi a gasar kasar Premier League ta Ingila, wasu na ganin Liverpool ta fara jin kamshin lashe kofin a bana.
Tun a shekarar 1989, rabon da Liverpool da ta daga babban kofin gasar Ingila.
A yanzu haka ana ganin cewar kungiyar ta dauko hanyar lashe kofin, hakan ya biyo bayan babakeren da ta yi a saman teburin wasan bana na 2018/20 inda a ranar Alhamis ta bi Leicester City har gida ta lallasata da kwallaye 4 da nema a wasan mako na 19.
Liverpool karkashin jagorancin Cocinta Jugen Kloop, tana da maki 52, banbancin maki 13 tsakaninta da Leicester City, wacce take take biye da ita da maki 39.
A ranar Lahadi Liverpool za ta karbi bakoncin Wolverhampton a wasan mako na 20.
Facebook Forum