Rundunar ta bayyana haka ne a wajen wani taron kwamitin tattaunawa tsakanin Musulmi da Kirista da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja. Taron ya sami halartar masana da kuma kwararru ta fannin zamantakewa tsakanin mabiya addinai dabam dabam.
A cikin jawabinshi, darektan sashen ilimi na shelkwatar tsaro Navy kwamando Isa’ac Manklik ya bayyana cewa, koyi da soja wajen aiki tare a kowanne sashe zai taimaka wajen maido da kishin kasa. Yace akwai Kirista akwai Musulmi a cikin rundunar sojoji amma suna zaman lafiya suna kuma gudanar da ayyukansu ba tare da wata tsangwama ba, saboda haka yace kamata ya yi kasar tayi koyi da wannan.
A nashi jawabin sakataren babban masallacin Abuja Ibrahim Jega yace fadace fadacen da ake yi a Najeriya bashi da nasaba da addini sabili da bisa ga cewarshi dukan addinan biyu addinai ne na zaman lafiya.
Shima Archbishop Mathew Manoson Danguso na darikar Katolika a Kaduna, yace akwai bukatar sada zumunci tsakanin shugabannin addinai domin kara fahimtar juna.
Wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu El-hikaya ya kuma yi hira da shugaban kungiyar hadin kan matasan arewa Usman Gamawa, yace zaman lafiya baya dorewa sai da tarbiyantar da matsa daga iyaye, shugabannin al’umma da cibiyoyin bada shawari da jagoranci.