Ranar 11, ga watan Oktoban kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniyar ta ware domin yara mata a duniyar baki daya.
Wani kalubale da yake addabar ‘yan mata masamman masu shekaru goma zuwa goma sha hudu shi ne tilasta masu yin aure da wuri da iyayensu kan yi masamman a kyauyuka.
A wani bincike da aka gudanar an gano cewa kasar Nijar ce tafi aurar da 'yan mata tun shekarunsu basu kai ba lamarin da sau tari yakan haddasa cutar yoyon fusari ga ‘yan matan saboda rashin cewar shekaru basu kai ba.
Hafsatu yarinya ce mai shekaru goma sha hudu dake jihar Maradi wadda ta gujewa auren wuri. tana cewa sai ta kai shekaru goma sha takwas domin ta koyi sana'ar yi. Kafin tayi aure.
Isa Suleiman, jami'i ne a ma'aikatar dake kula da yara mata da rayuwar mata a jihar Maradi. Ma'aikatar tana kokari wajan ganin ba'a aurar da yaran da shekarunsu basu kai ba. Malam Isa ya kan tattauna da iyayen dake kokarin aurar da 'ya'yansu mata tun shekarunsu basu kai ba. Yana wayar masu da kawuna akan illar yin hakan.
Sabili da bayanan da Isa Suleiman, ya yiwa iyayen Hafsatu ya sa suka fasa aurar da ita yanzu sai ta kai akalla shekaru goma sha takwas.
Aikin Isa ya taimakawa Hafsatu da kawayenta da su ma yanzu maimakon su yi auren sauri suna koyon sana'o'in tunda iyayensu basu sasu makarantar boko ba. Ma'aikatar Isa ke daukan nauyin sana'o'in da yaran ke koyo tare da basu kayan aiki idan sun gama.