A wannan karon dandalin voa ya sami zantawa ne da jama'a da dama domin jin tabakin su dangane da tambaya kamar haka, shin ra'ayi ne ko soyayya ko kuma yanayin tattalin arziki ke sa jama'a da dama shiga wannan yanayi na aure?
Jama'a da dama sun bayyana mana ra'ayoyin su musamman ganin yadda lamarin ya sami karbuwa a wasu jahohin arewacin Najeriya kuma wasu ke niyyar fara aiwatar da shi a nasu jahohin.
Da farko mun sami kusan kashi saba'in a cikin dari da suka bayyana mana cewa a ganin su yanayin tattalin arziki ne ke tursasawa jama'a shiga irin wannan yanayi na aure domin kuwa a cewar su, da dama sun yi amma a yau basu ba kayan da suka amsa hannun gwamnati ya'alla sun sayar ko kuma an gane zambar cikin amincin da suka kulla aka kuma kwace kayan.
Har ila yau, kashi talatin da suka danganta lamarin da sanin yakamata domin kaucewa aikata mugayen ayyuka da kuma kare mutuncin kai sun nuna cewar akwai matsalar tattalin arziki da kuma wani lokacin rashin sa'ar abokin zama kan kai wasu ga rabuwa dan haka neman sake aure ta wannan hanya a cewar su ba wata matsala bace.
Saurari cikkakiyar hirar.