Kungiyar Arsenal a gasar Premier League din Ingila, ta kori kocinta Unai Emery, bayan da ta ce ya gaza tabuka wani abin a zo a gani.
Yanzu an nada mataimakinsa Freddie Ljungberg a matsayin sabon kocin kungiyar.
“Mun ce Freddie Ljungberg ya dauki ragamar tafiyar da kungiyar a matsayin kocin wucin gadi.” Inji darektocin Arsenal.
Korar ta Emery wanda ya kwashe kasa da shekara biyu yana jogarantar Arsenal, na zuwa ne, bayan da ya gaza samun kwakkwarar nasara a wasanni bakwai.
Rabon da kungiyar ta Arsenal ta ga irin wannan koma baya, tun a shekarar 1992.
Korar ta Emery ta biyo bayan lallasa kungiyar da abokiyar hamayyarta ta Eintracht Frankfurt ta kasar Jamus ta yi da ci 2-1 a gasar Europa.
A wannan kakar wasannin ta bana, Arsenal ta yi kunnen doki a wasanni biyar ta kuma sha kaye a guda biyu.
Facebook Forum