Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AREWA A YAU: Matakan Da A Ke Daukawa Kan Dawo Da Daliban Jihar Yobe Gida Daga Sudan - Mayu 24, 2023


Wasu dalibai daga Sudan
Wasu dalibai daga Sudan

Masu sauraro barkanmu da dawowa shirin da ya ke duba lamuran da su ka shafi yankin arewacin Najeriya mai jihohi 19 kama daga lamuran tsaro, kuncin tattalin arziki, tarbiyya, tarihi da sauran su.

Sabon shirin Arewa a Yau zai shiga yankin jihar Katsina can kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar don duba bukatun tsaro na jama’ar yankin. Daga nan sai shirin ya tafi can arewa maso gabas a jihar Yobe don jin irin matakan da a ke daukawa kan daliban jihar da a ka dawo da su gida daga kasar Sudan.

Wasu dalibai daga Sudan
Wasu dalibai daga Sudan

A yankin karamar hukumar Jibiya da ke jihar Katsina mutane na fama da barayin daji da su ka addabi wasu daga jihohin arewa maso yamma har da Neja a arewa ta tsakiya.

Muntari TBO na daga jama’ar yankin da ke cewa su na bukatar sauyin dabaru don tunkarar kalubalen.

Wakilin jihar Yobe a kasashen Larabawa wajen tura dalibai don koyo ilimi musamman hanyoyin kauce wa akidu masu muni Umar Abubakar ya ce su na shirin kaurar da daliban zuwa Masar don kar karatun na su ya samu tangarda gabanin dawo da salama a Sudan.

Saurari shirin:

AREWA A YAU EP 114 05 24 2023.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:43 0:00
XS
SM
MD
LG