Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC: Matsayar Da Gwamnonin APC Suka Cimma Bayan Ganawa Da Buhari


Adams Oshiomohle
Adams Oshiomohle

Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun gana da shugaba Buhari a fadar Aso Rock don tattaunawa kan hanyar cimma maslaha game da rikicin shugabancin jam’iyyar da ya kai ga shiga kotuna daban-daban.

Duk da kotun daukaka kara ta janye dakatarwar da a ka yi wa shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole har sai an gama sauraron shari’ar, babbar kotun Abuja kuma, a wani umarnin, ta ce mukaddashin sakataren jam’iyyar, Victor Giadom, ne zai yi rikon kwaryar jam’iyyar har sai an yanke hukunci ko kuma sai idan kwamitin koli na jam’iyyar ya yanke matsaya.

Ganawar dai da shugaba Buhari, kamar yadda gwamnan Yobe kuma tsohon babban sakataren jam’iyyar, Mai Mala Buni ya bayyana, ta dauki matsayar dakatar da taron koli na jam’iyyar a ranar Talata don bin matakan sulhu.

Shi ma shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya ce dage baban taron shi ne matakin da su ka ga zai kai jam’iyyar ga cimma jituwa.

Da wakilinmu Nasiru Adamu El-Hikaya ya tambayi Mai Mala Buni ko me zai ce kan tunanin da wasu mutane ke yi na cewa ita ma APC ta kama hanyar shiga irin rikicin shugabancin da ya addabi PDP gabanin zaben 2015, da hakan ya kawar da Bamanga Tukur da nada Ahmed Mu’azu, sai Mai Mala Buni ya ce sam tsarin APC daban ne da irin na PDP don akwai masu tsawatarwa a jam’iyyar da ke daukar jagoranci daga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Za a jira a ga yadda za a warware wannan takaddama a dai-dai lokacin da babbar kotun Abuja da ke Maitama da kotun daukaka kara su ka sanya ranar 20 ga watan nan a matsayin ranakun duba karar ta APC.

Ga cikakken rahoton a sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG