Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Kira Don Sako Jami'an Kungiyar Red Cross Da Aka Sace A Afghanistan


Wasu Motocin Ma'aikatan ICRC Da Ke ‍Afghanistan
Wasu Motocin Ma'aikatan ICRC Da Ke ‍Afghanistan

Kwamitin kasa da kasa na kungiyar agaji ta Red Cross wanda ake kira ICRC a takaice yayi kira a yau Asabar da a sako ma’aikatansu guda biyu da aka kame a Arewacin Afghanistan a farkon wannan watan.

Wadanda aka kame din na cikin jerin ma’aikatan da ke raba kayan abinci ga manoman da talauci yayi wa katutu a arewacin yankin Jowzjan a ranar 8 ga watan Fabrairu, a yayin da aka yi musu kwanton baunan da ake zargin yan kungiyar Da’esh ne suka kai harin.

Kamar yadda jami’an tsaron Afghanistan suka ce, maharan sun kashe ma’aikatan kungiyar Red Cross din guda shida kafin su tafi da biyu daga cikin zuwa wurin da ba’a sani ba.

Kungiyar agajin ta dakatar da duk wasu harkokinta na taimakon jin kai a fadin kasar da miliyoyin mutane ke bukatar tallafin gaggawa sakamakon hare-haren 'ya'yan kungiyar Taliban da suka yawaita.

Monica Zanarelli shugabar ICRC ta fada a wani rubutaccen sako da ta bayar a yau asabar cewa, “Muna kira ga wadanda suka kama mana abokanan aikinmu da su tausaya su sako mana su lafiya ba tare da wani sharadi ba, kuma kada su saka rayuwarsu a cikin hadari. Ta kara da cewa “Bama son bakin cikin ya kara yi mana yawa.”

Zanarelli tayi kira ga hukumomi da jami’an tsaro da ke aiki a arewacin Afghanistan da su taimaka wajen ganin an sako ma’aikatan na kungiyar Red Cross lafiya. Wannan shine hari mafi muni da ya taba faruwa akan ma’aikatan kungiyar a cikin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG