Hukumar 'yan sanda na kasar Ingila ta fara binceke kan abunda ya faru a wasan da Tottenham ta lallasa Arsenal daci 2 - 0 cikin wasan daf da na karshe a Carabao Cup (Quarter Final) wasan ya gudana ne a filin wasa na Emirates Stadium ranar Laraba.
A yayin wasan anyi amfani da gorar (Plastic Bottle) inda aka jefi dan wasan Tottenham Dele Alli, a kansa a lokacin da ake mintuna na 73 da wasa.
Hukumar ta 'Yan sandan tace za tayi aiki kafada da kafada tare da Arsenal domin zakulo wanda ya aikata wannan laifin.
A bangaren kungiyar Arsenal tace zata tsawaita binceke kan faifayen Bidiyo, na CCTV dan gano yadda a bun ya faru, 'yan sanda sunce ya zuwa yanzu babu wani wanda aka kama kan wannan lamarin.
Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Ingila (FA) tace tana da masaniya akan wannan lamarin, kuma zata bada goyan baya ga hukumar ta 'yan sanda don aiwatar da bincekenta kan lamarin.
A bangaren kungiyar ta Tottenham Hotspur kocin kulob din Mauricio Pochettino, yace lamarin yazo da sauki domin babu wani rauni da dan wasan Dele Alli, ya samu amman ya kamata a dauki mataki domin kare faruwan wannan mumunar abu mara kyau.
Dele Alli dai shine dan wasan da ya jefa kwallo ta biyu acikin wasan.
Facebook Forum